Gawar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta baro birnin London, Birtaniya, da safiyar Yau Talata, zuwa garin Daura a Jihar Katsina, domin gudanar da jana’izar sa.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa an dauko gawar tsohon shugaban kasar ne a jirgin saman Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ne ke jagorantar tawagar gwamnatin tarayya da shirye-shiryen dawo da gawar tsohon shugaban kasar zuwa gida.

A jiya Litinin, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai karɓi gawar tsohon shugaban kasar a Katsina kafin a kai ta Daura don binne wa.
Ministan Watsa Labarai da Tsare-Tsaren Ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja.
Yanzu haka kuma rahotannin da Jaridar Kadaura24 ta samu daga Garin Daura, na tabbatar da cewa tuni aka Fara haka kabarin tsohon shugaban gidan a wani yankin daga cikin gidansa.
Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria
Wani ganau ya shaidawa majiyar Kadaura24 cewa bayan an Binne Muhammadu Buhari akwai kyakykyawan zaton za a katange kabarin nasa.
Yanzu haka dai jami’an tsaro sun yiwa gidan Buhari dake garin Daura a jihar Katsina kawanya, domin tabbatar da cewa an yi jana’izar ba tare da wata matsala ba.
Sai dai har yanzu gwamnantin jihar Katsina ba ta sana da a Inda za a gudanar da Sallar jana’izar Buhari ba.