Tsohon mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana cewa, tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da watakila bai tsira daga matsalolin lafiyarsa ba idan da ya dogara kacokan kan asibitocin Najeriya don samun kulawa.
Adesina ya yi wannan bayani ne a ranar Talata yayin wani shirin kai tsaye na musamman a tashar Channels Television domin karrama marigayi shugaban kasa.

Yayin da yake mayar da martani kan suka da aka yi wa Buhari saboda yawan zirga-zirgar da yake yi zuwa Birtaniya don neman magani a lokacin da yake mulki, Adesina ya kare wannan mataki, yana cewa lamarin ya shafi batun rayuwa ne.
“Buhari tun kafin ya zama shugaban kasa yana yin gwaje-gwajen lafiyarsa a London. Don haka ba wai lokacin da yake shugaban kasa kawai bane. Tun da dadewa yana yin hakan a can,” in ji Adesina.
Yanzu-yanzu: Karin bayani game da shirye-shiryen Jana’izar Buhari
A cewarsa, likitocin Birtaniya sun dade suna lura da lafiyar Buhari tun kafin zabensa a 2015, kuma sun san cikakken tarihin lafiyarsa.
Ya ce zaben ci gaba da neman kulawa a kasashen waje ya ta’allaka ne da kwarewar likitoci da kuma gazawar tsarin kiwon lafiya na Najeriya a lokacin.