Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar Dikko Radda ta ayyana litinin 14 ga watan yuli, 2025, a matsayin ranar hutu ga ma’aikatan jihar domin yin juyayin rasuwar tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari .

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Katsina Abdullahi Garba Farkari ya fitar .

InShot 20250309 102512486
Talla

Sanarwar ta ce Gwamnan Radda ya ba da hutun ne domin baiwa ma’aikatan jihar damar bin sahun sauran yan Nigeria wajen yin alhinin Buhari da kuma nema masa rahamar Allah Madaukakin Sarki.

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Sanarwar ta ce a madadin al’ummar jihar Katsina Gwamnan Radda na Mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan Muhammadu Buhari tare da Addu’ar Allah ya gafarta masa zunubansa ya Sanya shi a aljanna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...