Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa da tutocin Najeriya a ko ina a fadin Najeriya domin nuna alhinin rasuwar tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasa Bayo Onanuga ya fitar a Abuja .

Ya ce Shugaba Tinubu ya kuma baiwa mataimakinsa Kashim Shettima Umarnin da ya tafi birnin London domin Shirin dawo da gawar marigayi Buhari.
Sanarwar ta kara dacewa,tuni Bola Tinubu ya kira uwar gidan Buhari Aisha Buhari ta wayar tarho ya nuna kaduwarsa da mutuwar marigayin.
Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello
Tinubu yavce Najeriya ta yi rashin jajirtaccen mutum kuma dan kishin kasa.
Buhari rasu ne a yammacin Lahadi a London yana da shekaru 82 da haihuwa a duniya.
Ya rasu ya bar mace daya da ya ya guda 10 da jikoki da yan uwa.
Ya ya biyar ya same su ne da tsohuwar matarsa Hajiya Safinatu Yusuf,sai ya ya biyar da ya samesu da uwar gidansa ta yanzu Aisha Halilu.