Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya samu lambar yabo ta gwarzon shekara saboda ayyukan raya kasa a bikin ba da lambobi na gwarazan da suka yi fice a Afurka karo na 15.
A sakon da ya aika wa Kadaura24 Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce an ba wa Gwamna Yusuf lambar yabo ne a yayin bikin da aka yi a fadar nan mai tarihi ta Westminster Palace, House of Lords, London.
Mataimakin matakin garin birnin na London Mista Mete Coban, ya mika lambar yabon ganin irin ayyuka na raya kasa da Gwamna Yusuf ke yi don zamanantar da jihar ta Kano ta hanyar gina manyan hanyoyi da ayyuka na sabunta birnin da farfado da wasu muhimman gine-ginen al’umma.

Gwamna Yusuf ya samu wakilcin Usman Bala, mni, mai bashi shawara kan harkokin da suka shafi lamuran jiha da babban daraktan harkokin yada labarai da ke magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Da yake karbar lambar yabon amadadin gwamnan Kano Usman Bala ya bayyana farincikinsa yace wannan girmamawa da gwamnan ya samu ya nunar da irin jajircewar gwamnan wajen gudanarvda ayyuka ba tare da barin wani bangare ba.
“Wannan lambar yabo ta nunar da kwazon gwamna wajen ba da fifiko a samar da ababen more rayuwa da ke taba rayuwar miliyoyin al’ummar jihar Kano.”
Wannan lambar yabo da ake kira (African Achievers Award), an samar da ita ne bisa manufar karrama shugabannin da cibiyoyi daga kasashen Afurka da ke taka muhimmiyar rawa wajen jagoranci mai cike da samar da ci gaba.
Sauran wadanda suka samu wannan lambar yabo sun hadar da gwamnan jihar Benue da Sarkin Zolu na Afurka ta Kudu