Tinubu ya tura Shettima a ɓoye ya ziyarci Buhari a asibiti a London – Rahoto

Date:

Shugaban Nigeria Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, domin ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wani asibiti da ke London a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi masu tushe su ka shaida wa jaridar TheCable.

Tsohon shugaban ya dade yana fama da rashin lafiya, kamar yadda Empowered Newswire ta fara rawaito wa, amma ana ganin yana samun sauƙi a halin yanzu.

InShot 20250309 102512486
Talla

Shettima yan Addis Ababa, Habasha, a gayyatar Firayim Minista Abiy Ahmed Ali domin halartar ƙaddamar da shirin Green Legacy Initiative (GLI) na ƙasar ta Gabashin Afirka.

Sai dai Tinubu  wanda ke wata ziyara ta ƙasa a St Lucia — ya umurci Shettima da ya tafi London domin duba tsohon shugaban ƙasar.

TheCable ta fahimci cewa Shugaba Tinubu ya umarci Shettima da ya binciki yanayin lafiyar Buhari tare da tabbatar da an ba shi goyon baya har zuwa samun lafiya.

Shettima ya tashi daga Addis Ababa a daren Lahadi, inda ya isa London ranar Litinin kafin ya tafi wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin isar da saƙon Tinubu ga Buhari, in ji majiyoyin.

Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Shettima, ya tabbatar da cewa mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara London amma ya ce ba zai iya cewa komai game da manufar ziyarar ba domin bai san cikakken jadawalin tafiyar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An tsinci gawar wata dattijuwa mai shekaru 96 cikin rami masai a Kano

A ranar Alhamis al’ummar ƙauyen Sarai da ke ƙaramar...

Na riga Kwankwaso shiga harkokin Siyasa – Sanata Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jaridun Amurka sun bankado Tsare-tsare uku da sojojin Amurka ke yi don tunkarar Najeriya

Rahotanni daga wasu jaridun Amurka na bayyana cewa rundunar...

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...