Daga Isa Ahmad Getso
Al’umma da Malaman makaranta a unguwar Hotoron Arewa dake karamar hukumar Nasarawa sun koka bisa rashin kyawun hanya da magudanan ruwa da ya addabi yankin su musamman duba da shigowar damunar bana.
Mazauna yankin sun ce hakan na matukar barazana da hana ya’yan zuwa makaranta.

Umar Dauda daya ne daga cikin Mazauna Hotoron Arewa Unguwar Kwari ya ce suna fuskatar kalubale mai yawa idan akai Ruwa, inda ya ce tana kaiwa ga idan anyi Ruwa ya’yansu ba sa iya zuwa Makaranta.
“Mun jima muna kokawa bisa yadda hanyar mu ta lalace wanda mun yi iya kokarin mu wajan gyaran hanyoyi da magudanan ruwa Amma hakarmu bai cimma ruwaba”. Umar Dauda
Ya ce har kudi-kudi suka hada a kungiyance domin gyaran magudanan ruwan, amma Sai da su ka gama gyaran mamakon ruwan Sama da aka Samu a shekaran jiya ya Maida masu aikin baya.
Umar Dauda a madadin al’ummar unguwarsu ya na kira ga gwamnatin jihar Kano ta Mai girma Abba Kabir yusuf da shugaban karamar hukumar ta Nasarawa da a kai masu dauki dan kada karatun yaran su ya sami matsala.