Daga Zakaria Adam Jigirya
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya naɗa fitaccen ɗan wasan Super Eagles, Ahmed Musa, a matsayin Darakta Janar na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars a ranar Juma’a.
Gwamnan ya ce an nada Ahmad Musa a mukamin ne domin ƙarfafa ƙungiyar tare da inganta rawar da take takawa a fagen wasanni, musamman yayin da ake shirin shiga sabon zangon gasar Firimiya ta Najeriya.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.

Sanarwar ta bayyana cewa an zaɓi Ahmed Musa ne saboda kwarewarsa da tarihin nasarori a duniya da kuma irin gudunmuwar da ya taɓa bayarwa wa Pillars a baya.
Sanarwar ta ce Wannan matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na farfaɗo da harkar wasanni a jihar, tare da jawo masu zuba jari da raya matasa ta hanyar ƙwallon ƙafa.
Ga jerin sunaye mutane 17 da gwamnan ya nada a matsayi wadanda za su dafawa Ahmad Musa.
1. Ali Muhammad Umar (Nayara) – Chairman
2. Salisu Mohammed Kosawa – Member
3. Yusuf Danladi Andy Cole – Member
4. Idris Malikawa Garu – Member
5. Nasiru Bello – Member
6. Muhammad Ibrahim (Hassan West) – Member
7. Abdulkarim Audi Chara – Member
8. Muhammad Danjuma Gwarzo – Member
9. Mustapha Usman Darma – Member
10. Umar Dankura – Member
11. Ahmad Musbahu – Member
12. Gambo Salisu Shuaibu Kura – Member
13. Rabiu Abdullahi – Member
14. Aminu Ma’alesh – Member
15. Safiyanu Abdu – Member
16. Abubakar Isah Dandago Yamalash – Media Director I
17. Ismail Abba Tangalash – Media Director II