Masarautar Gaya ta sauke Usman Alhaji daga Sarautar Wazirin Gaya

Date:

Majalisar Masarautar Gaya da ke Jihar Kano, ta sauke Alhaji Usman Alhaji, daga Sarautar Wazirin na Gaya.

Masarautar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa Jami’in yada labaran shiyyar Gaya, Munzali Muhammad Hausawa, ya sanya wa hannu kuma ya aikowa Kadaura24 a yammacin yau Laraba, inda aka bukaci al’umma da su dau wannan bayani da muhimmanci tare da daukar matakin da ya dace.

InShot 20250309 102512486
Talla

A wata wasika da aka aikewa tsohon mai rike da sarautar, wanda kuma shi ne tsohon Sakataren gwamnatin Kano a lokacin gwamnatin Ganduje, Masarautar ta bayyana cewa an janye sarautar ne saboda wasu dalilai da ba za a iya kauce musu ba, kuma matakin ya fara aiki nan take.

Haka kuma Sakataren Masarautar Gaya, Alhaji Bello Halilu, ya ce Masarautar na matukar godiya da irin gudunmawar da Alhaji Usman Alhaji, ya bayar da kuma jajircewarsa a lokacin da yake rike da mukamin Wazirin Gaya.

Sanarwar ta kara da cewa, Masarautar ta yaba da goyon bayan da Alhaji Usman Alhaji, ya baiwa harkokin masarauta da kuma kokarinsa wajen inganta al’adun gargajiya da tarihinta.

A ƙarshe sanarwar ta ce wannan mataki na nuna jajircewar Masarautar wajen kare mutunci, kimar sarauta da adana martabar tsarin gargajiya bisa ga al’ada da dabi’un da aka gada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...