Guguwar iska mai ƙarfi ta yi barna a ƙaramar hukumar Bunkure da ke Jihar Kano, inda ta lalata gidaje da dama.
Daily Trust ta rawaito cewa lamarin ya faru ne a ƙauyukan Sakafalle-Jalabi da Zangon Buhari, duk a yankin Kulluwa na ƙaramar hukumar, wanda ya bar mutane da dama ba tare da matsuguni ba.

Rufin gidaje da aka yi da ƙarfe (zinc) sun yi barna, haka kuma wasu gidajen da aka gina da tubalin kasa da siminti sun rushe sakamakon ƙarfin iskar da ta tashi a ranar Litinin.
Ko da yake ba a rasa rai ba, an yi asarar dukiyoyi masu yawa a yayin guguwar.
Fadan daba ya sa an hade Sallar Magariba da Isha’i a wata unguwa Kano
Jami’in yaɗa labarai na ƙaramar hukumar, Labaran Garba, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa babu wanda ya rasa ransa.
Wakilin Hakimin Bunkure, Nasiru Umar, ya kai rahoton lamarin a hukumance ga Sarkin Rano, Alhaji Isa Umar.
A yayin da yake bada umarnin a tattara cikakken rahoto game da lamarin domin mikawa majalisar ƙaramar hukuma don daukar matakin da ya dace, Sarkin ya shawarci mazauna ƙauyukan da abin ya shafa da su ɗauki matakan kariya daga irin waɗannan masifu.