Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Shugabann karamar hukumar Wudil Hon. Abba Muhammad Tukur ya ɗauki nauyin karatun ɗalibai mata 33 domin su karanci aikin ungozoma don inganta Lafiyar mata masu juna Biyu a yankin.
Bayan daukar nauyin karatun nasu har su Gama ya mikawa ɗaliban takardar samun gurbin karatu ta kwalejin koyar da harkokin aikin ungozoma dake Kano. Wannan kuma kari ne kan ɗalibai mata Goma da tuni suka Fara karatun.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Babban sakataren yada labaran shugaban karamar hukumar Nura Mu’azu Wudil ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Sanarwar ta duba da muhimmancin ilimin ya’yan mata shi ne yasa gwamnatinsa ta ware kudade masu yawa don ba su Ilimi da kuma kawo karshen yawan samun mutuwar mata masu dauke da juna biyu.
Hon. Tukur ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na cigaba da fito da duk wani tsari da zai inganta rayuwar mata da kananan yara da ma lafiyar al’ummar Wudil baki daya, inda ya ce hakan ba za ta samu ba har sai an sami ƙwararrun mata da za su ba da tasu gudunmawar don cimma manufar da aka sanya a gaba.
Fadan Daba a Birnin Kano, Laifin Waye? – Barr. Hadiza Nasir
Tun lokacin da Hon.Tukur ya Zama shugaban karamar hukumar Wudil ya mayar da hankali wajen Gina da ɗan adam ta hanyar ba da Ilimi, Gwamnatinsa ta bayar da cikakken tallafin karatu ga dalibai guda 361 domin su yi karatun difloma a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, kuma a halin yanzu tana tallafa wa dalibai 141 da ke karatun Digiri a jami’ar.
A wani yunƙuri na tallafawa jin daɗin ɗalibai, Shugaban ya amince tare da bayar da kuɗi har Naira 600,000 don biyan kudin hayar Gidaje ga ɗaliban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi, sannan ya yi alkawarin ginawa ɗaliban filin da suka mallaka . Ya kuma himmatu wajen samar da ingantaccen ofis ga kungiyar Injiniyoyi ta Wudil domin bunkasa ayyukansu .
Hon. Tukur ya kuma bayyana aniyarsa na tallafa wa ayyukan gidauniyar bunkasa ilimi. Ya bayar da gudummawar ₦100,000 ga kungiyar masu sa kai ta karamar hukumar Wudil domin yabawa gudunmawar da suka bayar. Bugu da kari, ya bayar da gudunmawar ga cibiyoyin addini da na ilimi a fadin karamar hukumar:
Ya bayar da ₦400,000 ga Madarasatul Imam Ahmad Bin Musa, dake mazabar Wudil. Haka zalika ya ba da ₦200,000 domin kaddamar da kwafi 50 na kalanda a Madarasatul Mallam Sayyidi, Unguwar Sabon Gari. Sannan ya bayar da ₦200,000 ga makarantar Zakariyya’u Sulaiman Islamiyya, Utai.
Shugaban K/H Wudil ya taya Kungiyar Kwallon Kafa ta Kwankwasiyya Academy murnar Nasara da ta samu
Ya kuma ba da kyauta Naira ₦20,000 ga dalibai 8 da suka sauke Alqur’ani, don kara musu kwarin gwiwar cigaba da neman Ilimin addinin musulunci.
Wadannan ayyukan sun nuna irin kokarin da shugaban ya yi na tallafa wa ilimin zamani da na addinin Musulunci a cikin Karamar Hukumar.
A karshe, Hon. Abba Muhammad Tukur ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa gwiwar matasa maza da mata, inda ya sha alwashin ganin karamar hukumar ta Wudil ta ci gaba da samar da kwararru masu ilimi, don samun cigaba mai dorewa.