Daga Ibrahim Sani Gama
Kungiyar tsoffafin Daliban tsangayar makarantar Gwani Sabi’u dake karamar hukumar kura ta bukaci Gwamnatoci a matakai daban-daban da sauran masu hannu da shuni da tsoffafin daliban tsangayar da su kasance masu tunawa da tsangayar duba da gudunmawar da tanke bayarwa na tsawan shekaru sama da tamanin.
Shugaban kwamatin Dattawan kungiyar Alh salisu Biliya Takai ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a lokacin taron cikar Tsangayar shekaru 80 da kafuwa.

Alh salisu Biliya Takai ya ce,makasudun gudanar da taro na wannan shekarar shi ne, domin janyo hankalin mahukunta da sauran masu hannu da shuni da tsoffafin Daliban da su ka koyi karatu a tsangayar da su rika waiwayar makarantar domin taimaka mata da Kara ingantata.
Salisu Biliya Takai ya bayyana cewar yanzu haka akwai dalibai da dama da su ke jihohin kasar Nlnan da kasashen ketare har zuwa jami’ar Madina Wadanda makarantar ce ta yayesu.
Tinubu ya umarci ƴan Nijeriya da su yi azumin kwanaki 3
A jawabinsa Gwani Dr. Jafar Kura wanda kuma malami ne a jami’ar Yusuf maitama sule ya yi kira ga matasa da su jajirce wajen neman ilimi musamma na karatun Alkur’ani mai girma da sauran littafan addini domin sanin kansu a rayuwarsu ta yau da kullum da kaucewa shaye-shayen muggwan kwayoyi da fadan daba da kwacen wayoyin al’ummar,Wanda sau da yawa rashin ilimi yana ba da gagarumar gudunmawa.
Malam Surakatu Sabi’u Kura wanda daya ne daga cikin ‘ya’yan malam sabi’u kura wanda ya samar da wannan makaranta ya bayyana cewar, tsangayar tana bukatar Samar mata da guraren kwanan Dalibai saboda inda su ke ya yiwa tsangayar kadan, Wanda akwai bukatar kawowa makarantar dauki domin ta ci gaba da habaka da ilimantar da alumma sanin karatun Alkur”ani maigirma.
A nasa bangaren Gwani saidu sabiu kura yayi Kira ga alumma da su jajirce wajen sada zumunci tsakanin alumma Wanda haka Yana kawo daukaka da bunkasar Arziki da tsawan rai ga duk Wadanda suke sada zumunci tsakaninsu.
Haka zalika Gwani saidu sabiu kura ya yabawa Wadanda suka assasa wannan kungiya Wanda ya bayyana cewar,yin hakan zai taimaka gaya wajen sada zumunci tsakanin juna da yawan tunawa da murigayi malam sabiu kura daya Samar da wannan tsangaya shekaru sama da tamanin da suka gabata.
Daga karshe ya shawarci dukkannin tsaffin Daliban tsangayar da ma Wadanda suke makarantar har yanzu,da su zo a Kara hada hannu da karfe domin ci gaba assasa wannan kungiya da ita kanta tsangayar.