Ma’aikatar Noma da samar da Abinci ta Tarayya ta ƙaddamar da shirye-shiryen azumi da addu’a na kwanaki uku, domin neman taimakon Ubangiji wajen farfaɗo da bangaren noma a ƙasar nan.

A wata wasiƙa ta cikin gida da aka mai dauke da kwanan watan 11 ga Yuni kuma TheCable ta gani, Daraktan Gudanar da Ma’aikata na Ma’aikatar, Adedayo Modupe, ya bayyana cewa wannan ɗabi’ar ta ibada na neman taimako daga wurin Allah ne domin samun nasarar ƙoƙarin gwamnati na samar da abinci a ƙasar.
Ba Gaskiya a Labarin Rufe Kasuwar Singa Ranar Lahadi – Kwasangwami
Modupe ya ce dukkan ma’aikatan ma’aikatar ana tsammanin su yi azumi tare da halartar zaman addu’o’in.
“Wannan na da nufin gayyatar dukkan ma’aikatan Ma’aikatar Noma da samar da Abinci ta Tarayya zuwa wani zaman addu’a na musamman domin neman taimako da nasara wajen tallafawa ƙoƙarin gwamnati na cimma samar da abinci,” in ji wasiƙar.