Daga Rahama Umar Kwaru
Kungiyar Grassroot Care and Aid Foundation ta nemi Gwamnatin Jihar Kano da hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar mataki kan yawaitar matsalar kwacen waya da fadace-fadacen daba da ke jefa rayukan al’umma cikin haɗari.
Kadaura24 ta rawaito wannan na cikin wata wasika da shugaban ƙungiyar, Amb. Auwalu Muhammad Danlarabawa, ya aike wa Kwamishinan Harkokin Tsaro da sauran hukumomin tsaro na jihar, a ranar Asabar, 14 ga Yuni, 2025.

Kungiyar ta bayyana damuwa kan yadda matasa da mata da sauran marasa ƙarfi ke fuskantar barazana daga masu aikata laifuka, musamman a yankunan da aka fi samun fadace-fadacen daba da kwacen waya.
Dawo da Gwadabe ya Jagoranci Anti Daba Hanya ce ta Magance Fadan Daba a Kano
Ta bukaci a ƙara yawan sintiri da sa ido a wuraren da abin ya fi kamari, da kuma ƙarfafa dabarun tattara bayanan sirri tare da haɗin gwiwa da shugabannin al’umma da ƙungiyoyin matasa domin dawo da zaman lafiya.
Kungiyar ta kuma yaba da kokarin da hukumomin tsaro ke yi, tare da ƙarfafa gwiwarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.