Daga Nazifi Dukawa
Shugaban Kungiyar masu siyar da filaye, gidaje da kangwaye kuma mai kamfanin Annatija Properties Alhaji Naziru Tijjani Idiris ya karyata labarin rusau a garin rimin zakara da wani yayi zargi.
Alh Naziru Tijjani Annatija ya ce sanya Jan fenti alkhairi ne ya zo garin gwamnnatin jihar kano ce ta zo da karin cigaba a garin don cigaban da farantawa al’ummar yankin.

Ya ce waccen maganar ta tunani za a sake yin rusau a gari babu kamshin gaskiya a cikinta .
“Idan za a yi rusau ana rubuta alamar rushewa , Amma wanan kuma alama ce ta kidaya gidajen da kangwaye ce domin cigaban da tallafawa mazauna yankin”. Inji Naziru Tijjani
Al’ummar Rimin Zakara sun musanta zargin sake yin Rusau a garin, sun kori wanda ya yi zargin
Alhaji Naziru Tijjani Annatija ya ce idan mutane za su iya tunawa a baya gwamnan ya yi alkawarin kawo wutar lantarki yankin da asibiti da makaranta har ma da masallacin Juma’a.
“A halin yanzu kullum ma’aikatan gwamnnatin su na zuwa yankin don cigban da kawo ayyukan alkhairi a yankin don haka masu gidaje da filaye da kangwaye su kwantar da hankalinsu babu abun da zai faru.