Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya ta yi hasashen za a iya samun tsawa da ruwan sama a sassan Najeriya daban-daban daga ranar Lahadi 8 ga watan Yuni zuwa Talata 11 ga watan Yunin 2025.
Hukumar hasashen yanayin ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar a Abuja.

Inda ta ce za a iya samun wannan yanayin a a sassa da dama na kasar, da suka hada da jihohin Arewa maso yamma, Arewa ta Tsakiya, da Kudancin kasar.
A cewar NiMet, ana sa ran ranar Lahadi za a fara da ganin gajimare a wurare da dama, amma zuwa yammacin ranar yanayi zai canza .
Sarki Sanusi ya hori musulmi su hada kai don cigaban addinin musulunci
Hukumar ta bayyana cewa “da rana ko yamma, ana iya samun tsawa tare da ruwan sama a sassan Taraba, Adamawa, Katsina, Kano, Zamfara, Kaduna, Jigawa, Borno, Gombe, da Bauchi.”
“A shiyyar Arewa ta Tsakiya, da safe ana sa ran za a sami gajimare a yankin.
“Washegari kuma ana hasashen tsawa da ruwan sama a wasu sassan babban birnin tarayya, Neja, Nasarawa, Kwara, Kogi, Benue da Plateau.