Wani mai sayar da jarida, Lawan Muhammad Kiru, ya bayyana godiyarsa ta musamman ga Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf sakamakon bashi kyautar kujerar Hajji da ya yi a bana.
Kiru ya labarta wannan tagomashi ne ga tawagar manema labarai a birnin Makkah, kamar yadda kakakin Hukumar Alhazai ta Jiha, Suleman Dederi ya fitar a yau Asabar.

Dederi ya ce Kiru ya labarta wa manema labarai yadda ya saba da gwamna Yusuf sakamakon sayen jarida da ya ke yi a hannun sa a birnin Abuja, kimanin shekaru 30 da su ka gabata.
Kwamishina Waiya ya yi wa Gwamna Abba, Kwankwaso da al’ummar Kano Barka da Sallah
A cewar Kiru, gwamna Abba ya tuna da shi ne bayan da wani da ya zo wajen sa sayen jarida, su ka tattauna akan gwamnan, shi ne ya kai masa (Gwamna Yusuf) labari.
Nan take kuwa, in ji Kiru, gwamna Yusuf ya tuna da shi har ma ya bashi kyautar kujerar Hajji domin ya sauke farali.
“Mafarki na ya zama gaskiya. Ina matukar godiya ga Mai Girma Gwamna bisa wannan dama da ban taba samun irin ta a rayuwa ba,* in ji Kiru.