Hajjin bana: Gobarar ta tashi a otel din wasu Alhazan Nigeria a Makka

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hukumar kula da Alhazai ta Najeriya ta tabbatar da cewa daukacin alhazan Najeriya 484 da gobara ta shafa a otal dinsu da ke titin Shari Mansur a birnin Makkah suna cikin koshin lafiya.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 12pm agogon saudiyya a ranar Asabar.

IMG 20250415 WA0003
Talla

Maniyatan jirgin yawo da kamfanonin Nigeria shida suka kai ne suke zaune a Otal din mai suna Imaratus Sanan. Duk da fargabar da aka shiga, hukumar NAHCON ta ce ba a sami an asarar rayuka ba, kuma an kwashe dukkan alhazan lafiya zuwa Mina.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa daukacin alhazan Najeriya 484 da gobara ta shafa a otal dinsu da ke titin Shari Mansur a Makkah suna cikin koshin lafiya.

Shekaru 30 bayan rabuwarsu: Yadda Gwamnan Kano Abba ya baiwa ɗan tallan jarida kyautar kujerar Hajji

Bayan afkuwar lamarin, Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman, tare da rakiyar Kwamishinonin hukumar sun ziyarci wurin.

Da yake nuna damuwa yayin ziyarar, Farfesa Abdullahi ya ba da umarnin mayar da alhazan da abin ya shafa cikin gaggawa zuwa wani sabon masauki.”

InShot 20250309 102403344

Ya kuma jajanta wa alhazan da abin ya shafa, yana mai tabbatar da cewa hukumar za ta ba da duk wani tallafi da suke bukata.

NAHCON ta kuma yaba da matakin gaggawar da hukumar bayar da agajin gaggawa ta Saudiyya ta dauka da hadin kan ma’aikatan otal wajen Shawo kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...