Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero ya bukaci Gwamnan jihar kano Alh. Abba Kabir Yusuf da Shugaban Kasa da su cigaba da bijiro da ayyukan alheri ga al’umma.
Sarkin ya yi wannan jawabi ne a sakonsa na barka da sallah ga Gwamnati da al’ummar jihar Kano da musulmi baki daya.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran Sarkin Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Kadaura24.
Ya kuma bukace su da su cigaba da jaddada tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma lafiyarsu, inda ya yi addu’ar Allah ya cigaba da taimaka musu domin cika alkawarukan da suka yiwa al’umominsu.
Da dumi-dumi: Sarki Sanusi Fadi Matsayarsa Kan Hawan Sallah Babba
Alhaji Aminu Ado Bayero daga nan ya yi fatan al’umma za su cigaba da yi wa shugabanni addu’oin fatan alheri da kuma yin biyayya a gare su domin gabatar da ayyukan cigaba.
Da ya juya ga Limamai da Malamai kuwa, mai Martaba Sarkin ya gode musu bisa yadda su ke yin addu’oi da wa’azi da huduba akan Allah ya cigaba da gyara zukatan al’umma musammam Matasa.
Ya taya alhazan da su ke kasa mai sarki murnar sauke farali a wannan shekara tare da yin kira a gare su da su yi wa kasarmu da jihohinmu addu’oin dorewar Zaman lafiya da karuwar arziki da Kuma kwanciyar hankali.
Ya bukaci wadanda Allah ya horewa yin layya da suci, suyi kyauta su Kuma bayar da sadaka kamar yadda yake a koyarwar sunnar Annabi Muhammadu (SAW).