Wata maniyyaciya ƴar Najeriya mai suna Hajiya Zainab daga Jihar Plateau ta mayar da kudi har dala $5,000 da ta tsinta ga mamallakinsu, wani Dan kasar Rasha a ƙasar Saudiyya.
Kudin dai ya kai kimanin naira ₦8,240,000 bisa sauyin kudi na ₦1,648 ga kowace dala ɗaya, Hajiya Zainab ta tsinci kudin ne a Masallacin Harami da ke birnin Makkah a ranar Talata.

Hukumar Kula da Ayyukan Hajji ta Ƙasa (NAHCON) tare da Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Filato karkashin jagorancin Hon. Daiyabu Dauda ne suka tabbatar da wannan ci gaba.
“Ta nuna hali na gaskiya da amana ta hanyar mayar da dala $5,000 da ta tsinta a Masallacin Harami ga mamallakinsu. Wannan babban aikin kirki ne sosai!
“Abinda ta yi ya nuna halayen gaskiya, amana da tausayawa — muhimman dabi’u ga Musulmi. Allah ya sa labarinta ya zama abin koyi ga wasu don su kwaikwayi wannan hali nata na koyi,” in ji Dauda.