Matatar man fetur ta Dangote ta sanar da ƙarin ragin farashin kifar man fetur
Sabon farashin yanzu ya fara daga Naira 875 zuwa Naira 905 kowace lita, ya danganta da yanki.

Jadawalin sabon farashin ya nuna, Legas: Naira 875, Kudu maso Yamma N885, Arewa maso Gabas: N905, Arewa maso Yamma da ra Tsakiya: N 895, da Kudu-maso-Kudu da Kudu-maso-Gabas: 905.
Farashin ya nuna ragin N15 kowace lita a duk yankuna da gidajen mai na abokan hulɗar matatar.