Daga Saminu Ibrahim Magashi
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin daukar nauyin karatun wasu daga cikin dalibai yan asalin jihar a jami’ar International University of Africa dake kasar Sudan.
Mataimakin Gwamnan jihar Kano Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Shugabannin jami’ar wadanda suka kawo ziyara Kano karkashin jagorancin shugaban jami’ar Farfesa Hatim Usman Muhammad Khair.

” Mun yi farin ciki da ku ka kawo mana Wannan ziyarar kuma muna baku tabbacin gwamnatin jihar Kano za ta kulla yarjejeniya da wannan jami’ar ta hanyar tura ɗalibai don su yo karatu mai inganci”.
Ya ce suna da labarin yadda jami’ar ta shahara wajen koyar da harkokin addinin musulunci, don haka a kokarin gwamnatin Kano na tura ya’yan talakawa don su yi karatu za su tura ɗalibai daga jihar Kano don su yo karatu mai inganci.
Gwamnatin Kano ta magantu kan batun sayawa sarki Sanusi motocin Miliyan 670
Da yake nasa jawabin Jagoran shugabannin jami’ar international University of africa dake kasar Sudan Farfesa Hatim Usman Muhammad khair ya ce sun kawo ziyarar sake jaddada alakar zumunchi da mutanen Kano a wani kudiri na farfado da jami’ar tunbayan yaqin da ya barke a Kasar ta Sudan a shekarun baya.
Ya yabawa gwamnatin jihar Kano bisa yadda ta yi alkawarin hada kai da jami’ar don ilimantar da daliban jihar Kano a jami’ar.
Ya ce jami’rtasu tana da dumbin dalibai a Nigeria musamman jihar Kano hakan ya sa su ka zabi jihar a farkon wannan ziyara, inda ya bayyana cewa sun baiwa gwamnatin Kano kyautar gurbin karatu na ɗalibai 22 a jami’ar.
Ya kuma kara da cewa suna bukatar gwamnatin ta tura musu dalibai, inda ya yi alkawarin jami’ar za ta yi ragi na mussamman ga gwamnatin.
Adai ziyarar tasu sun Kai ziyara wajan muhimman mutane ciki har da Babban limamin Kano Farfesa Sani Zaharadden da mahaifiya sarkin Kano na 16 malam Muhammad Sanusi II, da Farfesa Galadanchi.
A bangaren makarantu kuwa tawagar ta kai ziyara jami’ar Northwest da Kuma jami’ar Khairun duk a cikin wani yunquri na hadin guiwa da makarantun dan farfado da alaqar ilmi da ke tsakaninsu.