Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Kamfanin albarkatun mai na Nigeria NNPC ya sanar da fara bayar da man fetur kyauta ga masu ababen hawa a babban birnin tarayya Abuja da kuma jihar Bauchi.
A wata sanarwa da kamfanin ya aikowa Kadaura24, ya ce kamfanin zai raba man ne kyauta a wasu sabbin gidajen mai mallakin kamfanin da aka bude a Abuja da Jihar Bauchi.

Sanarwar ta ce ” NNPC ya sake bude sabbin gidajen man ne a kokarinsa na ganin ya saukakawa yan Nigeria sun sami man fetur cikin sauki kuma a kusa da su.
Gwamnatin Kano, za ta kula alakar Noma, kasuwanci da makamashi da kasar Morocco
” Za mu bayar da man ne ga masu motoci da babura, domin nuna godiya ga al’umma bisa irin hadin kan da suke ba mu a ko da yaushe”.
” A Abuja kan titin Airport Road za mu baiwa masu babura kimanin 200 lita 5 – 5 na man fetur kyauta, yayin da kuma a sabon gidan man NNPC dake Kano – Ningi Road mu ka riga muka bayar da kyautar man ga kwastomomi da suka fara zuwa sayan mai a wurin mu a ranar 17, ga watan Afirilun 2025″.