Daga Buhari Ali Abdullah
Wata guda kafin fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa kasa mai tsarki don gudanar da aikin hajjin 2025, rikici ya barke a hukumar kula da alhazai ta kasa (NAHCON) yayin da mambobin hukumar suka nuna rashin jin dadinsu da salon jagorancin shugaban hukumar Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
Rahotanni sun nuna cewa mambobin kwamitin wadanda kuma kwamishinoni ne a hukumar, sun rubuta takardar koken na su ga mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, inda suka zargi shugaban da karya ka’idojin sayen kayan aiki a hukumar da kuma kin yin komai a bayyane wajen tafiyar da harkokin a hukumar.

Koken na zuwa ne makonni kadan bayan da kungiyar ma’aikatan NAHCON ta yi zargin rashin samar da walwala ga ma’aikatarn, sai dai hukumar ta musanta zargin .
Takardar koke da aka aikewa mataimakin shugaban kasar ta samu sanya hannun dukkan mambobin kwamitin da ke wakiltar shiyyoyi 6 na kasar nan da kuma wakilan majalisar koli ta harkokin addinin musulunci (NSCIA) da kungiyar Jama’atul Nasril Islam (JNI).
Don tabbatar da an kai wancan koke ofishin mataimakin shugaban kasa jaridar Daily trust ta tuntubi mai magana da yawun Shettima, Stanley Nkwocha, ta wayar salula, amma bai amsa kiran wayar ba kuma bai amsa sakon kartakwana da aka tura masa ba a ranar Litinin.
Mun gamsu da yadda malamai da daliban su ka koma makarantu – Gwamnatin Kano
Amma biyu daga cikin masu koken sun tabbatar da cewa ofishin mataimakin shugaban kasa ya karbi takardar.
Wadanda suka sanya hannu akan koken sun hada da: Farfesa Muhammad Umaru Ndagi (Arewa ta Tsakiya), Alhaji Abba K. Jato (Arewa-maso-Gabas), Shaykh Muhammad Bn Uthman (Arewa-maso-Yamma), Hajiya Aishat Obi (Kudu-maso-Gabas), Hajiya Zainab Musa (Kudu-Kudu), Dr Tajudeen Abefe Oladejo (Kudu-Yamma) da Farfesa AdezAdiwabola (South-mejifo), Farfesa AdezAdiwabola (South-mejifo), Farfesa AdezAdiwabola (South-mejifo) Fodio (JNI).
Sai dai hukumar ta ce tana gudanar da aiyukanta ne bisa ka’idojin da suka kafata, kuma babu wanda aka mayar da shi gefe kamar yadda ake zargi.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne ya nada Farfesa Abdullah Sale Usman a watan Agustan 2024, inda ya gaji Jalal Ahmad Arabi.