Shugaban Hukumar kula da aikin hajji A ta Najeriya (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya ce babu wata baraka da ta Kunno kai a hukumar.
Farfesa Abdullah Sale ya bayyana hakan ne a lokacin da yake mayar da martani kan wani labari da aka fitar wanda ke nuni da cewa wasu mambobin kwamitin zartarwa na hukumar sun rubuta takardar koke akan sa ga mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, inda suka zarge shi da rashin da’a, da karya ka’idojin yin sayan kayan aiki a hukumar.

Abdullahi Sale ya yi watsi da labarin, inda ya ce an yi labarin ne domin haifar da rudani a hukumar, yana mai cewa hukumar na da mambobin kwamitin zartarwa guda goma sha tara sabanin ikirarin.
Sabon Rikici ya Kunno Kai Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Nigeria NAHCON
Ya ce, “Mambobi biyu ko takwas din da suka rattaba hannu kan takardar koken ba za su iya sauya komai ba saboda kwamitin ya kunshi mambobi goma sha tara .
“NAHCON tana da mambobin kwamitin zartarwa na hukumar guda 19, hudu daga cikinsu na dindindin ne kuma su ke da alhakin gudanar da ayyukan yau da kullum na hukumar, hudun su ne shugabanni kuma kwamishinonin, sauran 15 kuma na wucin gadi ne masu ba da shawara.
“Ba su da hurumin kula da yadda ake gudanar da ayyukan ofis ko kuma yadda ake gudanar da ayyukan yau da kullum a hukumar, abun da doka ta ba su dama shi ne su a matsayinsu na ‘yan kwamiti su rika gudanar da taro a duk watanni uku don duba ayyukan da Hukumar ta gudanar a wannan lokaci da kuma yanke hukunci da dai sauransu.