Daga Aliyu Danbala Gwarzo
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya baiyana kaduwar sa da rasuwar malamin addinin Musuluncin nan, Sheikh Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi.
Dutsen Tanshi ya rasu ne a juya Alhamis da daddare a garin Bauchi, inda a safiyar yau Juma’a aka yi jana’izar sa.
A wata sanarwa da Kakakin shugaban, Bayo Onanuga ya fitar a yau Juma’a, Tinubu ya ce rasuwar Dutsen Tanshi doke ta girgiza al’umma duba da yadda ya dora miliyoyin matasa akan hanyar addinin Islama.

Tinubu ya kuma yabawa ƙoƙarin marigayin wajen adawa da tsaurin ra’ayin addini da ƴan Boko Haram ke yi, musamman a farkon fitowar su.
A karshe Tinubu ya taya iyali da al’ummar jihar Bauchi da ma kasa baki daya alhinin rasuwar, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya kuma badq haƙurin rashin sa.
Tinubu ya kuma horo matasa ɗaliban ilimi da su yi koyi da irin rayuwar ilimi da marigayin ya yi.
Dambarwar Rivers: AIG Gumel ya gamu da fushin Sufeto Janar na yan sandan Nigeria
Haka shi ma tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce ya kadu sosai da samun labarin malamin, inda ya bayyana shi a matsayin jigo wajen yada addinin musulunci.
Tsohon gwamnan jihar Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ma ya bayyana rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi a matsayin babban rashi ga al’ummar Musulmi baki daya.
Dukkaninsu sun yi wa malamin fatan samun Rahamar Allah subhanahu wata’ala.