NNPP Tsagin Kwankwaso ta yi Rashin Nasara a kotu

Date:

Daga Habiba Bukar Hotoro

 

Rikicin shugabancin da jam’iyyar NNPP ke fama da shi ya ɗauki wani sabon salo, yayin da babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta yi watsi da ƙarar da bangaren da ke biyayya ga Sanata Rabi’u Kwankwaso ya shigar gabanta, wanda ke neman kalubalatar sahihancin shugabancin jam’iyyar a ƙarƙashin wanda ya kafa ta, Cif Dr. Boniface Aniebonam, da kuma shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr. Agbo Major.

Shari’ar da Dr. Ahmed Ajuji da wasu mutane 20 da su ka shigar, inda su ke roƙon kotun ta ba su hurumin kwamitin amintattu na jam’iyyar NNPP (BoT) da shugabancinta, ciki har da Barr. Tony Christopher Obioha, Comrade Oginni Olaposi (Sakataren kasa), da Cif Felix Chukwurah (Mataimakin Shugaban Kasa).

InShot 20250309 102403344
Talla

Masu ƙarar dai sun buƙaci kotun ta hana wadannan jami’an gudanar da taro, ko gudanar da babban taron jam’iyyar na kasa, suna masu cewa an kore su daga jam’iyyar NNPP.

Sai dai a wani hukunci da ya yanke, mai shari’a M.A. Hassan ya ce kotun ba ta da hurumin shiga cikin karar, inda ya tabbatar da cewa rigingimun cikin gida-kamar shugabanci da kuma batun zama mambobin jam’iyya babu ruwan kotu da tsoma baki a ciki.

Gwamnan Kano ya bayyana dalilin da yasa ya sake dawo da Sarkin Gaya

Da wannan hukunci, kotun ta yi watsi da duk wani sassauci da masu da’awar su ka nema, inda ta tabbatar da cewa shugabancin Dr. Agbo Major na NNPP shi ne halastaccen dake da ikon sa ido kan al’amuran jam’iyyar.

Shi kuma Dr. Agbo Major yana tsagin su Boniface ba tsagin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...

Dalilin Kwankwaso na kin shiga Hadakar ADC

Jam'iyyar NNPP ta ce abin da ya sa ba...