Daga Maryam Muhammad Ibrahim
Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga matasa da su guji son zuciya da gaggawar neman cimma burikansu ta kowacce hanya.
Kwamishinan ya yi kiran ne a lokacin da ya gana da wata tawaga ta ƙungiyar F10 Initiative da ta ziyarce shi a ofishinsa.

Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa-hannun SDaraktan ayyuka na Musamman na ma’aikatar yaɗa labarai, Sani Abba Yola ya ce Kwamishinan ya ce matasa su riƙa haƙuri da biyayya, tare da wadatuwa da abin da Allah ya ba su. Ya kuma nuna cewa duk wani ci gaba na rayuwa yana buƙatar juriya da sadaukar da kai.
A cewar Waiya, matasa su ne ginshikin al’umma, saboda haka gwamnati za ta ci gaba da tallafa musu. Ya kuma yaba wa ƙungiyar F10 Initiative saboda ayyukanta na inganta rayuwar al’umma.
Gwamnan Kano ya bayyana dalilin da yasa ya sake dawo da Sarkin Gaya
Daga ɓangarensu, Daraktan ƙungiyar F10 Initiative, Abbas Abdullahi Yakasai, ya ce ƙungiyarsu ta ƙunshi ƙungiyoyi 50, waɗanda suka haɗu don ba da fifiko ga ci gaban Jihar Kano.
Ya kuma yaba wa Kwamishinan saboda rawar da yake takawa wajen inganta harkokin yada labarai.