Gwamnan Kano ya bayyana dalilin da yasa ya sake dawo da Sarkin Gaya

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa karbar kaddarar da Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Abdulkadir Gaya ya yi shi ne dalilin da yasa ya sake dawo da shi kan karagar mulkin Masarautar.

” Hakuri juriya da karbar kaddarar da ka yi lokacin da aka bayyana sauke ka daga kan karagar mulkin Masarautar Gaya shi ne babban dalilin da Allah ya kalla har ya sake dawo da kai”.

InShot 20250309 102403344
Talla

Gwamnan Kano ya bayyana hakan ne lokacin da Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Abdulkadir Gaya ya kai masa ziyarar Barka da Sallah.

Gwamnan Kano ya yi alwashin kawo karshen matsalar ruwa a masarautar Rano

A wata sanarwa da Babban Daraktan yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aikowa Kadaura24, ya ce gwamnatin ya yaba matuka da yadda Sarkin ya karbi kaddara.

“Abun da ka yi ka tabbatar wa duniya cewa kai mutum ne mai karbar kaddara a yadda ta zo maka, kuma hakan ya kara tabbatar da nagartarka don haka kai shugaba ne abun koyi”.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnatinsa za ta cigaba da bujuro da aiyukan raya kasa da cigaban al’umma a Masarautar ta Gaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...