Guda cikin Hadiman Tinubu ya ajiye mukaminsa

Date:

Dr. Hakeem Baba-Ahmed, mai ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, ya yi murabus, kamar yadda jaridar Daily Trust ta samu labari daga ingantattun majiyoyi.

Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun tabbatar jiya cewa tsohon kakakin kungiyar dattawan Arewa (NEF) ya mika takardar murabus dinsa kusan makonni biyu da suka gabata.

InShot 20250309 102403344
Talla

Daily Trust ta rawaito cewa majiyoyin sun ce Dr. Baba-Ahmed bai bayyana dalilan murabus din na sa ba, sai dai kawai ya ce yana da nasaba da dalilai na kashin kansa.

Duk da haka, a lokacin hada wannan rahoto, ba a tabbatar ko fadar shugaban kasa ta amince da murabus dinsa ba, in ji Daily Trust.

An nada Baba-Ahmed a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa a Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a watan Satumba na 2023.

Gwamnan Kano ya bayyana dalilin da yasa ya sake dawo da Sarkin Gaya

A cikin watanni 17 da suka gabata, ya wakilci fadar shugaban kasa a taruka daban-daban na jama’a, ciki har da wani taron kasa da aka shirya mai taken: “Karfafawa Dimokuradiyyar Najeriya: Hanyar Kyakkyawan Mulki da Ingancin Siyasa,” wanda aka gudanar daga 28 zuwa 29 ga Janairu, 2025, a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...