Daga Abubakar Sabo
Shugabar kwamitin yi wa daurarru afuwa a jihar Kano, Hajiya Azumi Namadi Bebeji, ta bukaci al’umma musammam madawata da su ringa taimakawa mutanen da ke zaune a gidajen gyaran hali, domin rage masu damuwar da su ka tsinci kan su a ciki.
Hajiya Azumin ta bayyana hakan ne lokacin da ta ke mika shanu goma sha biyu da da shinkafa da kayan miya wanda gwamnan Kano Kano Abba Kabir Yusuf ya samar masu don yin shagalin bikin Sallah karama.

Ta ce yin hakan a zo a lokacin da ya kamata kasancenwar sauran al’umna da ke zaune a gidajen su a cigaba da yin shagulgulan Sallah.
Waiya ya raba kayan Sallah da kudi ga matasan Kano da su ka tuba daga harkar daba
Ta kuma daurarrun za su cigaba da ganin canjin da ba su tsammata a ko da yaushe.

Anasu bangaren gidajen ajiya da gyaran halin na jihar Kano ta bakin mai magana da yawun su CSC Musbahu Lawan kofar nasarawa sun nuna godiya da Jin dadin su.
Yayin mika shanun shugabar kwamitin Azumi Namadi ta Sami rakiyar wasu daga cikin ‘yan kwamitin na yiwa daurarru afuwa.