Kwankwaso ya gana da Ɗalibai 300 da ya biyawa kudi sukai karatun kiwon lafiya

Date:

Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa

 

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce babban abin da ya kamata shugabanni su sanya gaba a wannan lokaci shine ciyar da rayuwar al’umma gaba, musamman marasashi.

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin taron shekara na daliban da su ka karanci aikin likitanci a tsarin Kwankwasiyya su dari uku su ka shirya.

Kwankwaso ya kuma godewa Likitocin bisa yadda su ka rika ciyar da rayuwar al’umma gaba da tallafawa marasa karfi.

IMG 20250330 WA0005
Sakon Barka da Sallah

Da yake jawabi shugaban Likitocin na tsarin Kwankwasiyya Dakta Baballe Sale Kibiya ya ce sun shirya taron ne domin hada kan wadanda Sanata Kwankwaso ya biya musu kudi suka yo karatun kiwon lafiya a ciki da wajen kasar nan.

” Mun kai akalla mu 500, kuma mun zo ne mu nunawa jagora cewa bai yi asarar kudaden da ya kashe mana muka yo karatu ba, kuma za mu cigaba da tallafawa rayuwar al’umma domin cika burin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso”.

Sallah: Gwamnan Kano ya ba da tallafin kayan abinchi da shanu ga daurarru

Shi kuwa kwamishinan ma’aikatar kimiyya da Fasaha na Kano Dakta Yusuf Ibrahim kofar Mata da ya kasance shugaban kungiyar daliban da sukai karatu a tsarin na Kwankwasiyya wato Kwankwasiyya Scholers cewa ya yi, duk wani wanda ya samu ci gaba a tsarin na yana da kishin samar da ci gaba a Kano dama kasar nan baki daya.

InShot 20250309 102403344
Talla

A nasa jawabin mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi na biyu da mai kula da harkokin lafiya a masarautar Kano Dakta Sha’awa Alhaji Sa’id ta wakilta cewa ya yi sarkin jan hankalin likitocin ya yi da su ci gaba da rike aikin su bisa gaskiya da tsaron Allah.

Taron ya samu halartar shugaban majalisar dokokin Kano Ismael Jibril Falgore da malaman addini da sarakuna dana manyan makarantun gaba da sakandare da dai sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalibai 22 sun kammala karatu da daraja ta 1 a bikin yaye ɗalibai na farko na Jami’ar Baba-Ahmed Kano

Jami’ar Baba-Ahmed, Kano ta gudanar da bikin yaye ɗalibai...

Rundunar Sojin Amuruka ta kammala tsara yadda za ta kawo wa Nigeria hari

  Rundunar sojin Amurka da ke Afirka, AFRICOM, ta gabatar...

Kalaman Trump: Gwamnatin Nigeria ta Fara tattaunawa da Gwamnatin Amuruka

Gwamnatin Najeriya ta ce a gwamnantance tana tattaunawa da...

Ba zan bar Siyasa ba har lokacin da zan bar Duniya – Mal Shekarau

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ce...