Ku hukunta wadanda su ka kashe mana mutane, kuma ku biya mu diyya – Gwamnan Kano ya fadawa na Edo

Date:

Daga Aliyu Danbala Gwarzo

 

Gwamnan jihar Edo Monday Okpebholo ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano bisa abin da ya faru na kisan gillar da wasu batagari suka yi wa Hausawan Arewa a yankin Uromi dake jihar Edo wadanda yawancinsu yan Kano ne.

Gwamna Okpebholo ya bayyana hakan ne a yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Kano a ranar litinin

Ya ce sun zo Kano ne shi da tawagarsa domin mika sakon ta’aziya kan kisan gillar da aka yi wa yan asalin kano a Edo da kuma tabbatar da cewa za’ayi adalci.

IMG 20250330 WA0005
Sakon Barka da Sallah

Gwamnan ya ce a yanzu haka an kama mutane 14 da ake zargin su na da hannu wajen kashe hausawan yan asalin Kano kuma suna tsare a yanzu haka.

Gwamnan na Edo ya ce ba dan ana hutun sallah karama ba ,da tuni an mika mutanan Abuja kamar yadda babban sifeton yan sandan Najeriya ya ba da umarni .

Ya tabbatarwa mutanan Kano cewa , za’ayi adalci a wannan lamari da ya faru a Edo.

“Mahaifina ya zauna a Hotoro da Gyadi Gyadi ,kuma Ina yawan zuwa Kano tun Ina matashi,a dan haka ba zan bari a cutar da Kano da mutananta ba”Inji gwamna Okpebholo

Anasa jawabin gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nuna takaicinsa kan abin da ya faru a jihar ta Edo ga al’ummar hausawan na Kano, ya na mai cewa za su hada kai da gwamnan na Edo domin tabbatar da adalci.

Haka kuma gwamna Yusuf ya godewa gwamnan na Edo Monday Okpebholo a bisa yadda ya nuna damuwa da kuma matakan da ya dauka na tabbatar da adalci ciki harda dakatar da ayyukan yan sintiri da aka samar ba bisa ka’ida ba a jihar.

Gwamnan na Kano ya ce , a madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ya na bukatar a nunawa duniya mutanan da aka kama domin kowa ya gansu, sannan a kaisu kotu, ya na mai kira ga gwamnan na Edo da ya jagoranci biyan diya ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Gwamna Yusuf ya kuma ce zai jagoranci raka gwamnan zuwa kananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya domin jajantawa iyalan mafarautan da aka kashe a jiharsa.

Daga nan gwamna Yusuf ya sake rokon jama’ar Kano musamman matasa da su guji daukar doka a hannunsu.

Ya kuma ce a yanzu mutanan Kano sun zura ido suga irin adalcin da za’ayi kan kisan gillar da akayiwa Hausawan na Arewa a Edo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...