Daga Rahama Umar Kwaru
A wani yunƙuri na taimako da jin-ƙai ga iyalan abokan karatu da su ka rasu, ƙungiyar tsoffin ɗalibai na makarantar share fagen shiga jami’a, CAS Kano, aji na 2002, sun rabawa marayun Naira miliyan 2, 780,000.
An yi rabon tallafin ne ga marayun, su 73, a HARABAR makarantar a jiya Lahadi, inda yanayin ya haifar da koke-koke daga wasu ƴan ƙungiyar da su ka halarci taron.
Da ya ke jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin walwala na ƙungiyar, Mansur Tukur Hotoro, ya yi bayanin cewa ƴan kungiyar ne su ka tara kuɗin har Naira miliyan 2,600,000 a cikin wata guda.

A cewar sa, bayan an yi lissafi da yawan marayun da kuma adadin kuɗin da za a baiwa kowanne, sai kungiyar ta cika Naira dubu 180 daga asusun ta domin adadin ya kai yadda ake so.
Ya ce duk mamata masu ƴaƴa ɗai-ɗai an baiwa marayun su Naira dubu 50, masu biyu-biyu an basu Naira dubu 40, masu uku-uku kuma an baiwa kowanne Naira dubu 35 da sauran su.
“Mun fara wannan tallafi ne a bara, 2024 domin tunawa da taimakon iyalan abokan karatun mu da su ka riga mu gidan gaskiya.
Bincike: Shin Sabon Hakimi ya shiga gidan sarautar Bichi kuwa ?
“Mun ci alwashin ɗorewa da wannan tallafi har bayan ran mu. Ina kira ga iyayen da aka barwa marayun nan da su rike su da kyau kamar yadda Addinin Musulunci ya yi horo da kuka da maraya.
“Mu na addu’ar Allah Ya gafarta musu, Ya kyauta makwanci, mu kuma Allah Ya kyauta namu zuwan,” in ji Hotoro.