Hukumar Shari’ah da haɗin guiwar kungiyar Wamy sun shiryawa wadanda su ka karbi Musulunci shan ruwa a Kano

Date:

Hukumar Shari’ah da haɗin guiwar kungiyar World Assembly of Muslim Youth (Wamy) sun shiryawa wadanda suka karbi addinin Musulunci shan ruwa a ranar Lahadi 23 ga Ramadan a harabar hukumar karkashin Jagorancin Mukaddashin Shugaban Sheikh Ali Danabba.

Hukumar ta Shari’a ta kuma ayyana ranar 15 ga Ramadan ta zama ranar da zata dinga shan ruwa da wadanda suka karbi addinin musulunci duk shekara.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan wayar da kai na hukumar shari’a ta jihar Kano Musa A Ibrahim (Best Seller) ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24.

InShot 20250309 102403344
Talla

Sheikh Ali Danabba ya kuma mika godiya ga gwamnatin jihar Kano a karkashin gwamna Abba Kabir Yusuf da Kungiyar World Assembly of Muslim Youth [WAMY] da suka basu gudummawa wajen shirya wannan taro.

Bincike: Shin Sabon Hakimi ya shiga gidan sarautar Bichi kuwa ?

Hakazalika shan ruwa ya sami halartar dukkanin mugabannin hukumar da mambobinta da kuma ma’aikatanta tare da shugabannin kungiyar Wamy da wasu manyan mutane da suka zo.

Shima wakilin shugaban kungiyar Wamy Alh Sanusi ya nuna jin dadinsa da yadda wannan shan ruwa ya faru, kuma ya tabbatar da cewar su kungiyar su ƙungiya ce ta taimakon addinin musulunci da musulmi a ko ina suke, kuma kungiyar zata ci gaba da wannan aikin alherin da izinin Allah.

Daga daga cikin wadannan yara da suka rabauta da addinin musulunci A’isha Suraj tace sun ji dadin yadda ake karrama da ake musu kuma suna jin dadi da yadda mutane suke jansu a jiki babu nuna banbanci ko kyama “Lalle addinin Musulunci addini ne mai dadi”

Shugaban hukumar Dr Sani Ashir ya godewa Allah da kuma kira ga masu hannu da shuni da su kawowa wadannan yara tallafi domin kara karfafarsu akan addini, sannan kuma ya bada tabbacin cewar wannan shirin an yi shine a kure amma shekara mai zuwa da yardar Allah za a ga shiri na musamman.

A karshe kwamishina na daya a hukumar Gwani Hadi yayi kira da al’umma da su zo domin auren wadannan yara domin babu irin kalar da ba’a da ita a wannan hukuma, yayi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan jihar da kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...