Kungiyar Gamayyar Direbobi ta Kasa ta rabawa marayu 51 abinchi da kayan sallah

Date:

Daga Kamal Umar Kurna

Kungiyar Gamayyar direbobin Najeriya ta bukaci wadanda su ke saya musu motoci domin yi musu aiki da su fito da wani tsari wanda zai dinga tallafar ‘ya’yan marayun cikin su wadanda su ka mutu sanadiyyar tukin mota.

Shugaban kungiyar na kasa Sadik Abdullahi Jada, shi ne ya bayyana hakan lokacin da kungiyar take rabon kayan sallah da abinci ga yara marayu 51 ‘ya’yan abokan aikin su da suka rigamu gidan gaskiya sanadiyyar tuki.

Shugaban ya ce kungiyar ta su wadda yanzu haka ta ke da mambobi sama da dubu 5 a fadin kasar nan, wannan shi ne karo na shida da ta ke gudanar da rabon tallafin ga marayun ‘ya’yan na su.

InShot 20250309 102403344
Talla

A cewar sa kungiyar ta su sun kasa ta ne gida 6 a sassan kasar nan, kuma kowane sashe yana gudanar da aikin sa da manufar tallafawa marayun abokan aikin su, wanda hakan ce ma ta sanya yanzu haka sun sayi fili mai girman fiye da fuloti 6 wanda suke burin samar da makaranta a ciki da wajen koyar da sana’ar dogaro da kai ga marayun na su, hakan ce ma ta sa suke bukatar iayayen gidan nasu da su tallafawa yunkurin nasu domin samarwa da ‘ya’yan nasu makom mai kyau.

Da yake nasa jawabin Shugaban kungiyar mai kula da shiyyar Kano, jigawa da Katsina, Mu’azu Umar Hadeja ya bukaci daukacin direbobin kasar nan da su shigo kungiyar ta su domin tallafawa rayuwar su da ta iyalan su koda basa raye.

Ba a taba samun dan shugaban kasa mai son mutane kamar Seyi Tinubu ba – Adamu Karkasara
Amina Lawan da A’isha Mohd, na daga cikin matan direbobin da aka mutu aka bar musu marayun ‘ya’ya, sun kuma bayyana cewa tun rasuwar mazajen na su har kawo wannan lokaci abokan sa direbobi sune suke ci gaba da daukar nauyin yaran da aka bar musu ta kowace fuska.

Daya daga cikin manyan bakin da suka jagoranci bayar da kayan tallafin da suka hadar da kayan sallah, takalma da abinci Alhaji Abdullahi Jada yayi kira ga mawadata da su mayar da hankali wajen tallafawa mabukatan da ke kusa da su domin neman dacewa a wajen Mahalicci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...