Kotu a Kano ta yankewa wasu ƴan TikTok ɗaurin shekara guda a gidan yari

Date:

 

 

Kotun Majistiri da ke zamanta a gini mai lamba 47 unguwar Norman’s land da ke ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano ta aike da wasu ƴan TikTok biyu gidan yari na shekara guda amma da zaɓin tara.

RFi ta rawaito cewa kotun ta samu ƴan TikTok ɗin biyu da laifin wallafa wasu bidiyo na rashin ɗa’a waɗanda suka ci karo da addini da kuma tarbiyyar jihar ta Kano.

InShot 20250115 195118875
Talla

Tun farko hukumar tace fina-finai ta jihar ce ta kame ƴan TikTok ɗin biyu waɗanda aka bayyana sunansu da Ahmad Isa da kuma Maryam Musa da suka fito daga unguwar Ladanai a yankin Hotoro na jihar, gabanin gurfanar da su gaban kotu.

Ta tabbata: NNPC ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Lauyan gwamnatin jihar Barista Garzali Maigari Bichi ya tuhume mutanen biyu da haɗa baki wajen aikata manyan laifuka baya ga wallafa saƙon da ya ci karo da tarbiyyar addini da kuma dokokin jihar ta Kano, laifukan da dukkaninsu suka amsa aikatawa.

20250228 181700

Mai shari’a Hadiza Muhammad Hassan da ta jagoranci zaman shari’ar ta aike da mutanen biyu gidan yari na shekara guda-guda amma da zaɓin tarar Naira dubu 100 kowannensu.

Haka zalika zaman shari’ar ya hori matasan biyu da su kasancewa masu ɗa’a da kuma bin dokokin jihar da addinin Islama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...