Abdulmumin Kofa ya ba da tallafin Azumi ga mutane 10,000 a Kiru da Bebeji

Date:

Daga Zakaria Adam Jigirya

 

Dan majalisar wakilai mai kananan hukumomin Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin Kofa ya tallafawa al’ummar Mazabar da kudade da sauran kayiyyaki domin saukaka musu a wannan wata na Ramadana.

Akalla mutane maza da mata akalla dubu 10 ne suka amfana da tallafin daga kananan hukumomin Kiru da Bebeji.

InShot 20250115 195118875
Talla

Wasu daga mutanen sun amfana da tallafin ₦200,000, wasu kuma ₦100,000, yayin da wasu suka samu₦50,000, wasu kuma ₦20,000, sai wasu kuma₦10,000.

Kotu a Kano ta yankewa wasu ƴan TikTok ɗaurin shekara guda a gidan yari

Haka kuma wasu matasa dubu 2 sun amfana da kayan sana’o’i domin su dogara da kawunansu .

20250228 181700

Da yake jawabin a yayin taron dan majalisar ya ce ya ba da tallafin ne domin saukakawa al’ummar yankin na sa.

Ya ce dama duk shekara yana gudanar da irin wannan rabo domin saukaka al’ummar yankin kananan hukumomin Kiru da Bebeji.

Kofa ya ba da tabbacin zai cigaba da tallafawa al’ummarsa, ko da ba lokacin Azumin watan Ramadana ba .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...