Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Birgediya Janar Kunle Nafiu a matsayin sabon Darakta Janar na Hukumar Kula da Hidimar Kasa (NYSC).
Kafin nadin nasa, Brigediya. Janar Nafiu shi ne Shugaban Ma’aikata na Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede. Haka kuma ya taba rike wannan mukami a lokacin marigayi Babban Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Raised Abiodun Lagbaja.
Sabon Darakta Janar na NYSC, Dan asalin Ileogbo, Karamar Hukumar Aiyedire a Jihar Osun ne.
Nafiu, wanda nadinsa ya fara aiki nan take, zai maye gurbin Birgediya Janar Yushau Ahmed.