Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Matatar mai ta Dangote ta bayyana cewa ta rage farashin man daga Naira N890 zuwa Naira N825 duk lita
Sanarwar ta ce Sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 27th February 2025.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ya ce ya rage farashin man ne sakamakon karatowar watan azumin Ramadan, don tallafawa yunkurin shugaban kasa na sasauta al’amura a Nigeria.
Fargaba: An tsaurara tsaro a Gidan Sarki na Nasarawa inda Aminu Ado Bayero ke zaune
Wannan ne dai karo na biyu a watan fabarairu da Dangote ya rage farashin man fetur bayan karin da aka samu kwanakin baya.