Yadda USAID ke ɗaukar nauyin Boko Haram —Dan Majalisar Amurka

Date:

Dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi ikirarin cewa Hukumar Raya Kasashe ta Amurka (USAID) ce ke ɗaukar nauyin kungiyoyin ta’addanci ciki har da Boko Haram.

Perry, dan jam’iyyar Republican mai wakiltar Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a taron sauraron ra’ayin na karamin kwamiti kan ingancin gwamnati a ranar Alhamis.

InShot 20250115 195118875
Talla

Kungiyar Boko Haram ta shafe sama da shekaru 15 tana kai hare-hare a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, inda ta kashe dubun-dubatar jama’a, ciki har da ‘yan sanda, da sojoji da fararen hula.

Hare-haren kungiyar sun yi sanadin mutuwar yara fiye da 300,000, da raba mutun miliyan 2.3 da gidajensu da kuma haifar da matsalar abinci da yunwa a yankin.

Abdulmumin Jibrin Kofa ya gabatar da kudirin kafa jami’a a Kano da wasu 15

A yayin zaman wanda ya mayar da hankali kan zargin karkatar da kudaden, Perry ya ce kuɗaɗen masu biyan haraji, “Dala miliyan 697 a duk shekara USAID ke kashewa, da kuma safarar kudaden ga kungiyoyin ISIS da Al-Qaeda da Boko Haram da ISIS Khorasan, da kuma sansanonin horar da ’yan ta’adda.”

Ya kuma ce hukumar ta USAID ta bayar da dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, inda ya yi zargin wata shaida ko da ke nuna gina makarantun.

Shugaba Donald Trump ya bayar da umarnin rufe hukumar ta USAID, kan zargin ta da cin hanci da rashawa a wani sako da ya wallafa.

Shi ma Elon Musk, abokin Trump, kuma shugaban ma’aikatar kula da ayyukan gwamnati, ya soki hukumar ta USAID, yana mai zargin cewa tana gudanar da ayyukan damfara.

Daga cikin masu sukar, Musk ya yi iƙirarin cewa USAID tana “aikin leƙen asiri kamar CIA” har ma da “binciken kuɗaɗen makaman ƙare-dangi, gami da COVID-19, wanda ya kashe miliyoyin mutane.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Iftila’i: An sanya dokar hana fita a Jigawa

An sanya dokar hana fita a Jihar Jigawa tare...

Gwamnan Kano ya bayyana abun da gwamnatin za ta yi a filin Idi

  Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar...

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...