Jaruma Maryam Malika ta roƙi kotu da ta tabbatar da sakin da mijinta ya yi mata

Date:

 

 

Jarumar masana’antar finafinai ta Kannywood, Maryam Muhammad, wacce aka fi sani da Maryam Malika, ta roƙi wata kotun shari’a da ke zamanta a Magajin Gari, Kaduna da ta tabbatar da sakin auren da tsohon mijinta, Umar ya yi mata.

Jarumar, wacce lauyanta A.S Ibrahim ya wakilta ta shaida wa kotun, s jiya Laraba cewa wanda ake kara ya furta saki na uku tun shekaru biyar da su ka gabata bayan ta nemi saki ta hanyar Khul’i (hakkin mace na ta nemi saki a Musulunci).

InShot 20250115 195118875
Talla

“Ya yi furuci na saki biyu ne bayan wanda na ke karewa ta shigar da kara a kotu ta na neman saki ta hanyar Khul’i.

“Kotu ta aika masa da takardar umarni kuma a kai ya rubuta saki na uku, inda wacce na ke karewa ta kuma ci gaba da harkokin ta ba tare da ta dawo kotu ta tabbatar da hakan ba,” in ji shi.

Shahararren Mai Horas da Kwallon Kafa a Kano a Rasu

Wanda ake tuhuma ba ya cikin kotu kuma bai aika da wani wakili ba.

Majiyar Kadaura24 ta Daily Nigerian ta rawaito Alkalin kotun, Kabir Muhammad, ya tambayi manzon kotun ko ya baiwa wanda ake kara takardar umarni sai ya amsa cewa wanda ake kara ba ya gida a lokacin da ya je kai masa takardun daga kotun.

Alkalin kotun ya umurci jami’an kotun da su sake aikewa wanda ake kara takardar umarni ta wasuhanyoyin sannan ya dage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Fabrairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...

Tinubu ka fadawa yan Nigeria Inda ka tsaya har kwana 5 bayan taron BRICS – ADC

    Jam'iyyar African Democratic Congress wato ADC ta soki Shugaban...

Da dumi-dumi: Yadda akai Jami’an tsaro suka kama ni -Danbello

Rahotannin sun tabbatar da cewa jami'an tsaro a Nigeria...