3rd Party Insurance Sabuwar Hanya ce ta Zaluntar Yan Nigeria – Inji Jaafar Jaafar

Date:

Daga Jaafar Jaafar

Aiwatar da dokar biyan mafi kankancin inshorar mota wadda ake kira “3rd Party Insurance”, manufa ce ta neman tatsar aljihun mutane.

Tun da ka ji ‘yansanda sun dage sai sun aiwatar, to kuwa ka san da dalili. Tsakani da Allah kashe-mu-raba kawai za su yi da kamfanonin inshorar, kai watakil ma wasu daga cikin manyan na da hannun jari a kamfanonin. Kwata-kwata ba kishin aiki ne ya sa ‘yansanda ke ta haƙilo ba.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ita inshorar mota wani kuɗi ne da za a biya wa duk motar da ake hawa a duk shekara ko duk wata. Amfanin kuɗin shi ne duk lokacin da aka buga maka mota, ko ka yi hatsari ko wani ibtila’i ya faru, to kamfanin inshora zai gyara, ko ya siya ma makamanciyar ta. Duk da cewa ‘yan Nigeria na biya in za su sayi ko za su sabunta takardun mota, amma ban taɓa jin wanda kamfanin inshora ya gyara wa mota ba, balle ya siya mai sabuwa.

A nan Ingila duk wata mu ke biyan inshorar mota, sai dai in ka zaɓi ka biya gaba ɗaya. Kuma kamfanonin ba sa ƙasa a gwiwa wajen gyara ko siya wa mutum sabuwar mota. Ni karan kaina duk watan duniya sai na biya wa mota ta inshora kimanin naira 260,000 kuma duk watan duniya sai na biya mata harajin hanya kimanin naira 30,000 kuma duk shekara sai na biya kimanin naira 110,000 domin duba lafiyarta.

Yanzu-yanzu: Dangote ya karya farashin man fetur

Amma me ya sa mutum zai biya inshora a Nigeria tunda kamfanonin inshora ba sa gyara ko siya wa mutum mota in ta yi haɗari? Rashin gaskiya ya yi mana katutu a Nigeria, tun daga kan hukumomi har jama’a. Baya da haka, a Nigeria ba a yin gwajin lafiyar mota (MOT test) duk shekara. A shekaru da su ka gabata da na san a Nigeria ana sa wa motar da bai kamata ta hau titi ba “OFF THE ROAD”, amma ba na jin yanzu ana yi. Dalilin haka shi ne, idan motar ta lalace a kan hanya, za ta iya jawo haɗarin zai iya sa wa a yi asarar rai.

A ƙasar Ingila idan sahihin garejin gwajjn lafiyar mota (MOT centre) bai tabbatar da lafiyar mota ba kuma bai ba da satifiket ba, to ba za ka hau motar ba. Duk motar da ba ta inshora ko MOT ko haraji, tana gittawa ‘yansanda za su gani a sikanar da ke motocinsu, kuma za su kama motar.

A ƙasashen da su ka ci gaba, idan motarka ta faɗa ‘pothole’ ta lalace, za ka iya neman gwamnati ta biya ka diyya. A Nigeria fa? A lokacin da ina Nigeria, zai wahala na je Kano daga Abuja sau uku ban fasa taya ko shakzoba ba.

Batun gaskiya shi ne, su kan su kamfanonin inshora a Nigeria sun san karya ce kawai. Domin idan tsakani da Allah za su riƙa biya, faɗuwar (risks) ta fi ribar yawa. Babu kamfanin kasar waje da zai yadda ya yi harkar inshora a kasar da ba a koyon tuki bisa kaida, ba a ƙayyade gudu a kan titi, babu kyamarar kama wanda ya wuce ƙa’idar gudu, babu alamu a gefe, babu zanen layi radau a kan tituna, sannan kuma ga ramuka fal hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...