A kokarinsa na inganta rayuwar al’umma maza da mata, Shugaban karamar ukumar Nassarawa Amb. Yusuf Imam Ogan boye ya bayar da tallafin kudaden ga na kimanin miliyan hamsin da tara da dari biyar a aljihunsa ba na gwamnati ba.
Kadaura24 ta rawaito wannan dai shi ne karo na biyu da shugaban karamar hukumar ta Nasarawa ya ke baiwa matasa maza da mata tallafi don su dogara da kawunansu.

Yayin da yake jawabi a wajen taron kudin Ogan boye ya ce yana ba da tallafin ne la’akari da mawuyacin hali da al’umma suke cikin, kuma yana ganin kudin za su taimaka musu su fara sana’o’i don su dogara da kawunansu.
” Ina fatan za ku yi amfani da wadannan kudade wajen inganta sana’o’in da kuke yi, wadanda kuma ba su da sana’a sai su fara, idan Allah ya sanyawa kudin albarka sai ku ga mun taimakawa kanku har ma ku taimaki wasu”. Inji Ogan boye
Gwamnan Kano Ya Tallafawa Matasa 340 Da Suka Kammala Makarantar Kiwo da Rainon Tsirrai
Kadaura24 ta rawaito wasu sun rabauta da mashina, wasu sun rabauta da kudade.
Kimanin mutanen dari da hamsin (150) ne suka sami dubu dari bibiyu (200,000). Mutane talatin (30) kuma suka rabauta da Naira dubu dari biyar (500,000) kowannensu.
Mata dari da hamsin (150) kuma suka rabauta da dubu ashirin kowanne su. Tare da bawa wasu daga cikinsu gudunmawar aure su biyar ta naira dubu dari bibiyu.
Duk wannan tallafi ya yi shi ne cikin aljihunsa don ya inganta rayuwar al’umma su samu abin dogaro a rayuwarsu.
Ga hotunan yadda rabon tallafin ya gudana: