Gwamnan Kano Ya Tallafawa Matasa 340 Da Suka Kammala Makarantar Kiwo da Rainon Tsirrai

Date:

Daga Sani Idris maiwaya

 

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya raba shanu, raguna, da kayan aikin lambu na zamani ga matasa 340 da suka kammala karatunsu a cibiyoyin kiwon dabbobi da rainon tsirrai a Jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24 ranar Laraba.

Gwamnan ya sanar da cewa kowane mutum cikin wanda suka kammala karatun zai samu bijimin sa biyu ko raguna biyu, tare da abincin dabbobin na watanni uku.

InShot 20250115 195118875
Talla

Gwamnan ya ce Wannan shiri, wani bangare ne na kokarin gwamnatinsa na rage radadin talauci da kuma karfafa gwiwar matasa jihar domin su zamo masu dogaro da kawunansu.

A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya jaddada cewa shirin na nuni ne da yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen inganta rayuwar matasa da samar da abinci, wadanda ke da matukar muhimmanci wajen tabbatar da ci gaban jihar Kano.

Yadda Gwamnatin Kano ta yi Rinton Aiki a Dawakin Tofa – Bincike

Wadannan matasa 340 su ne rukunin farko na dalibai da aka yaye a cibiyar kiwon dabbobi da rainon tsirrai da ke Bagauda a karamar hukumar Bebeji, biyo bayan bude cibiyar da gwamnati mai ci ta yi.

Gwamnan ya kara da cewa, an sake yi wa wasu matasa 340 rajista a karo na biyu.

“Daliban da aka yaye a wannan cibiya yanzu za su iya dogara da kawunan don inganta rayuwarsu da taimakawa wasu.

Gwamnan ya ja hankalin wadanda suka amfanan da su hada kai ta hanyar kafa kungiyoyin domin su rika tattauna yadda za su ciyar da sana’arsu gaba.

Ya kuma baiwa dukkanin wadanda suka kammala karatun aikin rainon tsirrai kayan aiki na zamani tare da jari na Naira 100,000 don tallafa musu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abubakar Bichi ya bada gudumawar motocin bas 13 ga jami’o’in Kano da taraktoci 11 ga yan mazabarsa

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Dan Majalisar tarayya mai wakiltar karamar...

Rikicin Sarautar Kano: Fadar Sarki Sanusi ta zargi magoya bayan Sarki Aminu Ado Bayero da kai farmaki Kofar Kudu

Daga Sani Idris Maiwaya   Rikicin Masarautar kano ya na neman...

Shugabannin Kasuwar Kanti Kwari sun shiryawa Gwamnan Kano Addu’o’i na musamman

Daga jafar adam Shugaban kasuwar Kantin Kwari Sharu Abdullahi Namalam...