Asibitin Aminu Kano ya yi martani kan rahoton cire mahaifar wata mata ba tare da yardar ta ba

Date:

 

Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, AKTH, ya musanta aikata wani laifi a aikin tiyatar da aka yi wa wata mata, inda ta yi tir da rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa a baya-bayan nan da ke nuna cewa sun yi ba daidai ba.

Kwanan nan kafafen sada zumunta sun cika da rahoton cewa matar ta samu matsala yayin tiyatar da asibitin ya yi mata tun a shekarar 2012.

Sai dai kuma shugaban asibitin, Farfesa Abdurrahman Sheshe, ya musanta zargin a matsayin maras tushe balle makama da kuma bata sunan asibitin.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya gabatar da cikakkun bayanai daga fayil ɗin matar a yayin taron manema labarai din.

A wata zantawa da manema labarai a ranar Talata a Kano, Sheshe ya bayyana cewa an fara kwantar da majinyaciyar a asibiti a watan Fabrairun 2012 kuma an yi mata tiyatar ceton rai a watan Oktoba na wannan shekarar sakamakon matsalolin da ta fuskanta lokacin nakuda.

Yadda Gwamnatin Kano ta yi Rinton Aiki a Dawakin Tofa – Bincike

Ya bukaci kafafen yada labarai da jama’a da su nemi sahihan bayanai daga majiyoyi masu inganci kafin su gabatar da ra’ayoyinsu kan batutuwa.

“Rahoton cewa wai an cire wa wata mata mahaifa bisa kuskure sannan aka ji wa jariri ciwo ba wai karya bane kadai, har da ma bata sunan asibitin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...