Tsagaita wutar: Yarjejeniya 11 da aka cimma tsakanin Hamas da Israel

Date:

Daga Ahmad mansur Al-Jazeera, Fassarawa zakariyya Adam jigirya

Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma abar alfahari ce ga Falasɗin, sannan kuma ƙasƙanci ce ga mamayar Isra’ila:

1. Ficewar sojojin Isra’ila gaba ɗaya zuwa iyakokin yankin daga dukkanin sassan Gazza.

2. Buɗe iyakar Rafah, da ficewar sojojin Isra’ila gaba ɗaya daga wurin.

3. Tura marasa lafiya zuwa waje don samun magani.

4. Shigo da motoci 600 na agaji kowace rana, bisa tsarin jin ƙai da ƙasar Qatar ke kula da shi.

InShot 20250115 195118875
Talla

5. Shigo da tantuna 200,000, da gidaje masu yawo (Caravan) 60,000 don ba da mafaka cikin gaggawa.

6. Musayar fursunoni, da sakin fursunoni 1,000 daga Gazza, da ɗaruruwan fursunoni masu hukunci mai tsanani.

7. Sakin dukkan mata da yara ƴan ƙasa da shekaru 19 daga gidajen yarin Isara’ila

Ka rike shawararka ba ma so – Tinubu ga Sarki Sanusi II

8. Ficewa daga hanyar Nitsarim, da sansanin Filadelfiya a Gazza a hankali.

9. Komawar dukkan ƴan gudun hijira zuwa gidajensu, da tabbatar da yancin zirga-zirga a Gazza.

10. Hana jiragen sama tashi a saman Gazza na tsawon sa’o’i 8-10 a kowace rana.

11. Gyaran dukkan asibitoci, shigo da asibitocin wucin gadi, da ƙungiyoyin likitoci zuwa Gazza.

Dukkan wannan yana cikin mataki da zango na farko wanda zai ɗauki makonni 6, a madadin bayar da fursunoni Yahudawa 33 tsakanin waɗanda suke da rai da gawarwaki. Za a ci gaba da matakai na biyu da na uku don tattauna kan sauran fursunoni 66 da suke hannun ƴan tirjiya.

Zamuci gaba da bibiyar Yadda zata Kaya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Tinubu ya Iso Kano domin ta’aziyyar Dantata

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya iso jihar Kano...

ALGON ta Kano Sa’adatu Soja ta sami sabon matsayi a kungiyar ALGON ta Ƙasa

Daga: Aliyu Danbala Gwarzo. Shugabar karamar hukumar Tudunwada kuma ALGON...

Da dumi-dumi: Tinubu zai zo Kano

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu zai zo Kano ranar...

Tinubu ya sauya sunan jami’ar Maiduguri zuwa Sunan Muhd Buhari

Shugaba Bola Tinubu ya sauya sunan Jami'ar Maiduguri zuwa...