Ka rike shawararka ba ma so – Tinubu ga Sarki Sanusi II

Date:

Gwamnatin Tarayya ta mayar da martani kan kalaman Sarkin Muhammad Sanusi II na cewa ba zai taimaki gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ba wajen gyara manufofin gwamnatin da ke shafar ‘yan kasa.

Sanusi ya jawo cece-kuce a jiya Laraba a Legas a matsayin shugaba a taron lakca na tunawa da Gani Fawehinmi karo na 21.

InShot 20250115 195118875
Talla

A cewar Sarkin, ba zai taimaki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba saboda “ba su ɗauke shi a matsayin aboki ba.”

Sai dai a yau Alhamis, Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, a cikin wata sanarwa, ya ce gwamnatin tarayya ba ta bukatar shawara da ga Sarki Sanusi wajen aiwatar da ‘manufofinta masu kyau’.

Sanarwar ta ce ” tabbas a matsayinka na dan kasa kana da dama kayi tsokaci aka matakin da gwamnatin ta dauka, Amma ka sani nan gaba kadan yan Nigeria za su fara amfana da sauye-sauyen tattalin arziki da shugaban kasa Bola Tinubu ya kawo”.

Nasiru Ja’o’ji ya ziyarci mataimakin shugaban Kasa, Kashim Shettima

Ya nuna rashin jin dadinsa cewa sauye-sauyen da masana tattalin arziki na duniya, har da shi Sarkin amma yanzu ya na kushe su saboda wani ra’ayi na sa.

Idan aka yi la’akari da tarihin Sanusi a fannin tattalin arziki, ministan ya ce Sarkin yana da wani nauyi na musamman na bayar da gudunmawa mai inganci, maimakon kawo cikas ga sauye-sauyen da ake yi na samun ci gaba kawai saboda ya na jin haushin wasu “abokansa” a gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...