Hajin bana: Hukumar jin dadi alhazai ta Kano ta zamo zakara bisa samun yawan maniyata

Date:

Daga Maryam Muhammad Ibrahim

 

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta zamo kan gaba wajen karbar kudaden ajiya ga masu niyyar zuwa aikin hajjin shekara ta 2025.

Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa ne ya bayyana hakan a yau a lokacin da yake ganawa da jami’an alhazai na kananan hukumomi da jami’an gudanarwa na hukumar a dakin taro na hukumar.

Darakta Janar wanda Daraktan gudanarwa na hukumar, Alhaji Yusif A. Muktar ya wakilta, ya bayyana cewa, a yayin wani taron shirye-shiryen Fara aikin Hajji da aka gudanar kwanan nan a kasar Saudiyya, wanda ya samu halartar daukacin hukumomin alhazai na Jihohi, an amince da cewa jihar Kano ita ce a kan gaba wajen sayar da kujerun aikin hajji a fadin kasar.

InShot 20250115 195118875
Talla

Ya yabawa gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da take baiwa hukumar. Ya kuma bukaci jami’an alhazai na kananan hukumomin da su kara himma domin dorewar wannan gagarumar nasara.

Babban Darakta ya ba da tabbacin cewa za a yi duk wasu shirye-shirye da suka hada da sanar da masauki, abinci, motocin sufuri, da kula da lafiya, domin tabbatar da jin dadi walwalarsu alhazan jihar Kano a Saudiyya.

Ka rike shawararka ba ma so – Tinubu ga Sarki Sanusi II

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Sulaiman Abdullahi Dederi ya aikowa Kadaura24, ya ce a nasa jawabin, Daraktan Ayyuka na hukumar, Alhaji Muhammed Ghali Muhammed, ya shawarci jami’an hukumar alhazai na kananan hukumomi da su kasance cikin shiri domin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) za ta bayyana kudin aikin Hajji nan ba da jimawa ba. Ya nuna jin dadinsa ga hadin kan jami’an alhazai da masu kula da shiyyar suke bayarwa .

Daraktan fadakarwa na hukumar Alhaji Murtala Lawan Sani ya sanar da cewa hukumar za ta kaddamar da Bitar alhazai a mako mai zuwa a masarautar Rano. Ya bayyana cewa an zabi Masarautar Rano ne bisa la’akari da irin namijin kokarin da ta yi wajen tara yawan maniyata a bana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...