Shin ko kun san ƙi taimakon ɗansanda’ a Nigeria laifi ne?

Date:

Rundunar ƴansandan Najeriya ta tunatar da al’ummar ƙasar cewa mutanen da suka ƙi taimakon jami’anta a lokacin da suke neman ɗauki, na iya fuskantar hukuncin ɗauri ko kuma tara.

A cikin wani bayani da rundunar ta wallafa a shafinta na X, rundunar ta ce wannan na ƙunshe ne a sashe na 99 na dokar ƴansanda ta ƙasar ta shekarar 2000.

Talla

“Duk wanda aka kira domin ya taimaka wa jami’in ɗansanda wanda – a sa’ilin gudanar da aikinsa ke fuskantar cin zarafi ko hantara ko turjiya – sai mutum ya ƙi, ko kuma ya yi watsi da buƙatar taimakawa, to wannan mutum ya aikata laifi, wanda zai iya janyo a yanke masa tarar naira 100,000 ko ɗaurin wata uku, ko kuma duka biyun idan aka same shi da laifi,” kamar yadda bayanin ya nuna.

Iftila’i: Yan ɗaurin aure 19 daga Kano sun kone a hatsarin mota a Filato

Rundunar ƴansandan Najeriya ɗaya ce daga cikin hukumomin tsaro da kundin tsarin mulkin ƙasar ya dora wa nauyin tabbatar da doka a cikin al’umma.

Sai dai sau da yawa an sha kokawa kan yadda jami’anta ke gudanar da ayyukansu.

Wannan ne ma ya haifar da ɗaya daga cikin zanga-zanga mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar, inda a cikin shekara ta 2020 matasa suka gudanar da zanga-zangar domin nuna adawa da ‘zaluncin’ wani ɓangare na rundunar, wanda ake yi wa laƙabi da SARS.

Lamarin da ya yi sanadiyyar rushe ɓangaren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

NAHCON ta sanar da ranar da za a fara jigilar Maniyatan Nigeria zuwa kasar Saudiyya

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Hukumar kula da aikin hajji ta...

Hisbah ta rushe wajen da aka ce sawun Ma’aiki ya fito a jihar Kano

    Hukumar Hisbah ta kai samame tare da rushe wani...

ƴan siyasa ne su ka kashe Arewacin Nigeria — Inji Gwamna Uba Sani

Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ‘yan...

Shugaban Karamar hukumar Bagwai ya kaddamar da aikn gada ta sama da Naira Miliyan 160

Daga Shu'aibu Sani Bagwai   Karamar hukumar Bagwai a jihar Kano...